fidelitybank

Rikicin Rasha da Ukraine: Kimanin ƴan Najeriya 200 sun shiga Romania daga Ukraine

Date:

Ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen da ke maƙwabtaka da Ukraine, na ci gaba da karɓar ‘yan ƙasar da ke ficewa a dai-dai lokacin da yaƙi ke kara rincaɓewa.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta ce, ta na aiki da ofisoshin jakadancin ƙasashen Ukraine da Poland da Rasha da Romania da kuma Hungary, domin tabbatar da ganin an mayar da su gida.

Bayanai sun ce, ɗaruruwan ‘yan Nijeriya ne suka tsallaka kan iyakar Ukraine, inda ake sa ran kwashe su zuwa birane mafiya aminci, kafin mayar da su Najeriya.

Romania ta kasance daya daga cikin kasashen da suka karbi ‘yan Najeriya da ke zaune a Ukraine.

Jakadiyar Najeriya a Romania, Safiya Nuhu,ta shaida wa BBC cewa, ya zuwa yanzu sun karbi ‘yan Najeriya 200 inda suke kyautata zaton za su samu fiye da haka.

Ta ce,” Bisa la’akari da cewa Najeriya tana da dalibai da dama a Ukraine, don haka mun san cewa dole a samu karin mutanen da za su shigo kuma mu a shirye muke mu karbe su don taimaka”.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp