fidelitybank

Rikicin PDP: Gwanoni 3 na APC sun ziyarci Wike

Date:

Gwamnonin uku na jam’iyyar APC, Gwamna Babajide Sanwoolu na jihar Legas, Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti da Gwamna Rotimi Akeredolu, sun gana da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Fatakwal a ranar Juma’a.

Wannan taro dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ya barke a jam’iyyar PDP, ta samu labarin cewa, gwamnonin uku jakadu ne da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu ya aika, domin neman goyon bayan Wike.

Ana kyautata zaton jam’iyya mai mulki da kuma Tinubu na kokarin yin amfani da karfin da ke tattare da rikicin jam’iyyar adawa ne, domin neman goyon bayan Wike a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Idan dai za a iya tunawa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar ya ki amincewa da zabi Wike a matsayin abokin takararsa ko da an kafa kwamitin da zai zabi mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ya zabi Gwamnan Ribas.

Hakan dai ya janyo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar adawa. Da yake magana a taron, Fayemi ya ce;

“Za mu je Fatakwal ne domin ganawa da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar, amma mun yanke shawarar yin amfani da damar wajen kai ziyarar ban girma ga abokin aikinmu gwamnan jihar.”

Gwamnan jihar Ribas dai ya ci gaba da adawa da dan takarar jam’iyyarsa Atiku, tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana Okowa a matsayin mataimakinsa.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya yi tir da yadda jam’iyyar PDP da Atiku suka yi wa Wike markashiya, ya kuma shawarci dan takarar da ya tuhumi gwamnan.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp