fidelitybank

Rikicin PDP da APC: Mutum daya ya mutu a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai suna Abdullahi Isiyaku mai shekaru 37 a duniya, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da APC a karamar hukumar Maigatari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP ke gudanar da wani taro a Maigatari.

Shiisu ya bayyana cewa rikicin ya barke ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar PDP suka isa sakatariyar jam’iyyar APC da ke Gangare Quarters inda suka kai wa wani Abdullahi Isiyaku hari.

Ya ce an garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gumel inda daga baya daya ya mutu a lokacin da ake jinya.

Shiisu ya ce, an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a rikicin.

Ya ce an mayar da shari’ar zuwa ga SCID don yin bincike mai zurfi.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp