Rundunar sojin Isra’ila ta ce, tana tsammanin rikici a Gaza zai ci gaba da gudana a tsawon shekara ta 2024.
A wani saƙon sabuwar shekara, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra’ila Daniel Hagari ya ce an daidaita harkar tura dakarun soji don shirin tunkarar “faɗa na tsawon lokaci”.
Ya ce za a janye wasu dakaru – musamman ma sojojin wucin gadi – don ba su damar sake tattaruwa.
“Waɗannan gyare-gyare ana yin su ne don tabbatar da ganin an yi tsare-tsare da shirye-shirye da nufin ci gaba da yaƙi a shekara ta 2024,” in ji shi.
Ya ce wasu sojoji masu wucin gadi za bar Gaza “tun a wannan mako” don ba su damar “sake kintsawa gabanin wasu ayyuka da ke tafe”.
Mutum 21,978 – akasari mata da ƙananan yara ne – aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma’aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon Hamas. Ta kuma an jikkata mutum 56,697 a Gaza a tsawon wannan lokaci.
Adadin ya haɗar da na mutum 156 da aka kashe da 246 da aka ji wa raunuka a tsawon sa’a 24 da ta wuce, ma’aikatar ta ƙra da cewa.