Mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutum 85 a tsawon kwanaki da aka kwashe ana rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato.
Rikicin ya barke ne tun a ranar Litinni a yankin da ake yawaita samun rikicin kabilanci da addini a tsawon shekaru.
Har yanzu dai babu wasu sahihan bayanai da ke tabbatar da ainihin abin da ya hadasa rikicin.
Irin wannan rikici tsakanin makiyaya da manoma domin fansa abu ne da aka saba gani a kauyuka da dama da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Hukumar agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ta ce rikicin ya raba dubbai da muhallasu.