Kungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ce, ta sako wata ‘yar Isra’ila da ‘ya’yanta biyu da take tsare da su, tun bayan hare-haren da ta kai ranar Asabar a cikin Isra’ila.
Har yanzu ba a tabbatar da sanarwar da dakarun na rundunar Qassam ta Hamas suka fitar ba, kuma wasu kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun yi watsi da sanarwar, suna cewa da ma can ba a yi garkuwa da matar ba.
Tashar talbijin ta Aljazeera da ke Qatar ta yada wani bidiyo da ta ce yana nuna sakin matar da ‘ya’yanta ne.
A bidiyon, an ga wata mata tana tattara kayanta da na ƴaƴanta a filin Allah ta’ala, daidai kusa da wata katanga, ga kuma wasu mayaƙa biyu dauke da makamai suna mata rakiya.