Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Talatar da ta gabata ya dora laifin rashin nasarar zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar a matakin jihar.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke ne ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 403,371 inda ya kayar da gwamna mai ci Gboyega Oyetola wanda ya samu kuri’u 375,927 a zaben da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 30 na jihar.
Da yake nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya jaddada cewa jam’iyyar ta amince da shan kaye da gaskiya kuma ta koyi darasi mai kyau daga gare ta.
Sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zabe mai zuwa yayin da ya yi kira ga jam’iyyar adawa ta PDP da ta jira sakamakon babban zaben.
Ya ce, “Mun yi rashin nasara a gasar ba don ba za mu iya ba amma saboda rikicin ne ya haddasa shi. Mun yi gagarumin taron magoya baya kwanaki kadan kafin zaben a Osogbo. Mutum ba zai taba tsammanin za mu fadi zabe ba.
“Amma al’adar rayuwa ce ku rasa wani abu da kuke bukata sosai. Mun amince da shan kaye da imani kuma muna daukar darasi daga ciki.
“Kayewar Osun ko ta wace hanya ba ya nuna rashin nasararmu a babban zabe. Jiha daya kawai muka rasa daga cikin 22 da muke da su; ka ga har yanzu muna da karfi.
“Za mu zauna mu binciki kanmu. Dole ne mu tambayi kanmu abin da yake daidai da abin da ba daidai ba, me ke bukatar gyara,” inji shi.