Sam Ohuabunwa, jigo a jam’iyyar PDP, ya bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, da ya yi murabus idan har ta kawo karshen kiyayyar da ke tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Ohuabunwa ya yi wannan kiran ne a gidan talabijin na Channels.
Rahotanni sun ce Ayu ya amince ya yi murabus ne lokacin da aka zabe shi a matsayin Shugaban jam’iyyar a shekarar da ta gabata idan PDP ta zabi dan Arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Sai dai bayan fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP, ana sa ran cewa Ayu zai cika alkawarinsa ya bar kujerar dan Kudu a wani bangare na kokarin murde ra’ayin shiyya-shiyya a cikin jam’iyyar.