fidelitybank

Rikicin APC: Bafarawa ya caccaki El-Rufa’i a kan Tinubu

Date:

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan kalamansa na cewa akwai shirin yin zagon kasa ga nasarar da ake sa ran dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu zai samu.

Naija News ta ruwaito cewa, El-Rufai, a wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya yi ikirarin cewa akwai wasu abubuwa a Aso Rock da ke yiwa jam’iyya mai mulki zagon kasa da karancin kudin Naira a wani yunkuri na yin tasiri ga nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben.

Da yake mayar da martani da manema labarai a Abuja ranar Saturda, Bafarawa ya shaida wa gwamnan Kaduna cewa babu wani yunkuri na yi wa jam’iyyar APC zagon kasa ko kuma mai rike da tutarsa, Bola Tinubu.

Jigon jam’iyyar PDP ya bukaci El-Rufai da ya daina nanata cewa dole ne Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa mai zuwa, yana mai jaddada cewa Arewa ba ta goyon bayan dan takarar APC.

A cewar Bafarawa, El-Rufai ko wani ba shi da hurumin dora dan takararsa a kan wasu mutanen Arewa.

Karanta Wannan: Zan cigaba da tallata Tinubu – Buhari

Ya ce: “Ya nanata cewa dole ne Tinubu ya ci zabe, ko mutane sun so ko ba su so, sun riga sun ci zabe. Wa ya gaya masa cewa duk yankin Arewa yana goyon bayan APC?

“Wannan ra’ayinsa ne kawai, idan haka ne, ba shi da hurumin dagewa kan Arewa saboda kowa yana da dan takararsa.

“Yadda yake yiwa Tinubu kamfen haka muke yiwa dan takararmu kamfen.”

“Za mu firgita su, za mu fahimtar da su cewa kasar nan ta kowa ce, ita ma Arewa.”

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp