fidelitybank

Rikicin APC a Kano: Sifeto-Janar na Ƴan Sanda ya yi sammacin ɓangarorin Ganduje da Shekarau

Date:

 

Sifeto-Janar na Ƴan Sanda, Usman Alkali, ya gaiyace ɓangarorin da ke rikici a jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Kano.
A ƴan watannin da su ka gabata ne rikici ya ɓarke a APC a Kano, inda tuni jam’iyar ta dare gida biyu, lamarin da ya haifar da ɓangarori biyu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau.
A tuna cewa, ɓangaren Shekarau sun kai takardar ƙorafi zuwa ga ofishin Sifeto-Janar ɗin, in da su ke zargin tsarin Ganduje da kai hari kan ofishin Sanata Barau Jibrin a Kano.
Nan da nan suma ɓangaren Ganduje su kai kai ƙarar tsagin Shekarau gaban Sifeto-Janar ɗin a bisa zargin su Shekarau ɗin da tada zaune tsaye a jihar.
Waɗannan ƙorafe-ƙorafe ka iya zama dalilin da ya sanya Sifeto-Janar ɗin ya gaiyace su domin shawo kan matsalar.
Wakilin jaridar PlatinumPost ya gano cewa tuni wakilan ɓangarorin su ka isa shalkwatar ƴan sandan da ke gidan Louis Edet a Abuja yau Talata da safe.

legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...
X whatsapp