Daga jihar Ribas kuwa, har yanzu rikicin siyasa na cigaba da ruruwa, yayin da Gwamna Siminalayi Fubara zai fuskanci karin kalubale fiye da rikicin da ke faruwa da ‘yan majalisar da ke goyon bayan tsagin Wike.
Yanzu haka kungiyar kananan hukumomin ta kasa ALGON reshen jihar Ribas, ta zargi gwamna Fubara da rike kudaden da aka ware wa kananan hukumomi 23 na jihar.
Wannan mataki a cewar kungiyar ta ALGON, ya kawo musu cikas wajen gudanar da ayyukansu.
Shuwagabannin sun yi ikirarin cewa abin da Gwamnan ya yi daidai ne da soke kananan hukumomi a jihar.
Sun kuma nuna goyon bayan kiran tsige gwamnan da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Tony Okocha ya yi, wanda ya bukaci majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Martins Amaewhule ta fara yunkurin tsige gwamnan.
Da yake yiwa manema labarai jawabi Allwell Ihunda, shugaban ALGON na jihar kuma shugaban karamar hukumar Fatakwal ya ce Fubara ya ci gaba da rike kason kananan hukumomi 23 na jihar Ribas tun daga watan Afrilun 2024.