fidelitybank

Rikici ya rincabe tsakanin Indiya da Pakistan

Date:

Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren indiya da Pakistan na ƙaruwa, inda aka ruwaito cewa aƙalla mutum 26 sun mutu, 46 kuma sun jikkata a Pakistan bayan hare-haren sojojin Indiya.

A ɓangaren Indiya kuma, mutum 10 ne suka mutu yayin da 32 suka samu raunuka a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi sakamakon harin ramuwar gayya daga Pakistan.

Sojojin Indiya ne dai suka fara ƙaddamar da wani hari mai suna “Operation Sindoor” inda suka hari wurare tara da ke cikin Pakistan da kuma yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.

Wannan harin ya haifar da martani cikin gaggawa daga Pakistan, wanda ya janyo rikicin da ya fi kowanne tsanani cikin fiye da shekaru ashirin da suka gabata tsakanin ƙasashen biyu masu makaman nukiliya.

Shugabannin ƙasashen biyu na gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba domin tattaunawa kan rikicin.

Harin da Indiya ta kai da kuma ramuwar gayya daga Pakistan na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsanancin tashin hankali, bayan wani hari da aka kai a watan da ya gabata kan masu yawon buɗe ido a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi – wanda New Delhi ta ɗora alhakin hakan a kan Islamabad, sai dai Pakistan ta musanta wani hannu a cikin harin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar Laraba, gwamnatin Indiya ta ce dakarunta sun kai harin ne kan “wuraren ‘yan ta’adda da ke cikin Pakistan da kuma yankin Jammu da Kashmir da Pakistan ke iko da shi, inda ake shiryaw da kuma kaddamar da hare-hare a kan Indiya.”

leadership newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp