fidelitybank

Rikici ya lafa bayan Matasa sun yi wa DPO jina-jina da zargin kashe Matashi a Rano

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa an samu barkewar rikici a karamar hukumar Rano.

Lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin, wadanda ke ganin an hallaka baturen ‘yan sandan yankin, Baba Ali.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da rikicin a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ɗaya daga cikin mazauna garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Jiya akwai wani bawan Allah yana yawo a kan babur, sai aka kama shi aka kai shi wajen DPO, sai ya dake shi. Da ya ga dukan da ya yi masa, dukkan alamu ya jikkata sosai.” “Sai ya kai shi asibiti, daga bisani sai aka ce ya mutu da safe. Jama’ar gari sai suka tafi ofishin ‘yan sanda suna son su ɗauki fansa. Sai ‘yan sanda suka fara harba barkonon tsohuwa. Jama’a kuwa sai suka tayar da wuta. DPO kuma sai ya ɗauko bindiga ya harbe mutane biyu. Su kuma jama’a sai suka kona shi.”  Ya shaida wa manema labarai.

Rahotanni na nuni da cewa tuni aka sauya Baturen ‘yansandan yankin.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp