Tun daren jiya ake ta ce-ce-ku-ce, bayan da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba wanda aka kashe sama da mutane 1,400 a Isra’ila ‘ba haka kawai’ ya faru ba.
Kalaman sun jawo tsauraran kalamai daga ministan harkokin wajen Isra’ila, wanda ya ce “babu dalilin da zai haifar da irin wannan kisan kiyashi”.
Yanzu Isra’ila ta ce za ta ki bayar da takardar shiga ƙasar ga manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya.
Jakadan Isra’ila a Majalisar Gilad Erdan ya shaida wa kafafen yaɗa labaran Isra’ila cewa “Muna bukatar mu bai wa MDD mamaki.”
Ya ce shugaban Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kai Martin Griffiths ya so zuwa Isra’ila – kuma an hana shi.
“Ba zai iya zuwa nan yankin ba, kullum hukumominsu na buƙatar kawo sabbin mutane, musamman a irin wannan lokacin, ba za a amince masu ba.”


