Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan’adam sun ce, wani sabon rikici ya ɓarke a yankin Sweida na Syria inda aka kashe mutum sama da 110 a cikin mako guda na rikicin kabilanci.
Hukumar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce an kai wa ƙauyuka da dama hari ciki har da al-Ariqah inda aka ƙona gidaje.
Mayakan Bedwin da sauran masu taimaka masu sun janye daga Sweida amma sun kasance a wajen garin.
Rikicin ɗaya ne daga cikin manyan ƙalubalen da ke gaban sabon shugaban ƙasar ta Syria