Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta dakatar da Hajiya Maryam Mai-Rusau shugabar mata ta jihar bisa zargin ta da kare tsohon Gwamna Nasir El-Rufai kan cece-kucen da jihar ke fuskanta a baya-bayan nan kan basukan da ake bin jihar.
Kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na gundumar Badarawa/Malali ya bayyana a wata wasika a ranar Lahadin da ta gabata cewa dakatarwar ya zama dole saboda ta saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, musamman sashi na 21.2 (v).
Shugaban gundumar Ali Maishago da Zakka Bassahuwa ne suka sanya wa hannu tare da mika wa manema labarai a jihar.
An karanta a wani bangare kamar haka: “Saboda abubuwan da ke sama, a ƙasa akwai manyan laifuka inda dakatarwar ta dogara da su:
“Bata sunan Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani.
“Bayyana rigingimun jam’iyyar da ya bata sunan Gwamnan Jihar Kaduna ba tare da izini ba.”
Dakatarwar dai ta samo asali ne daga zargin bata sunan halayen Gwamna Uba Sani da kuma bayyana rashin izini na rikicin jam’iyyar da tsohon gwamnan.
A baya dai gwamnan Kaduna ya bayyana cewa ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga hannun wanda ya gada.