Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (INEC) ta bayyana cewa katin zabe na mutane miliyan 1,126,359 daga cikin miliyan 2,523,458 na dindindin da aka yi wa rajista ta internet tsakanin watan Yuni zuwa Disamba 2021 ba su da inganci.
Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Sa’idu Babura ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin INEC na jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.
“Bayan aikin tantancewa, an gano cewa daga cikin masu rajista 2,523,458 a fadin kasar nan, 1,390,519 suna aiki yayin da 1,126,359 ba su da inganci a jihar Zamfara 19,469 suna da inganci yayin da 13,600 suka lalace.” Ya kara da cewa.
“Wannan yana nufin kashi 44.6 na wadanda suka yi rajista tsakanin watan Yuni zuwa Disamba 2021 suna cikin rajista da yawa.”
Da yake karin haske, Kwamishinan Ma’aikatar Jihar ya ce, a Jihar Zamfara, a watan Disambar 2021, mutane 33,09 ne kawai suka yi rajista a layin, inda ya nuna cewa, 19,469 ne kawai ke aiki, yayin da 13,600 da ke wakiltar kashi 41.1% ba su da inganci.
Ya kara da cewa, akwai rumfunan zabe 2,516 a jihar a shekarar 2019, amma tare da karin rumfunan zabe 1,013, adadin ya kai 3,529.