Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana kudurinsa na ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP duk da raba gari da Atiku.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen ya fice daga jam’iyyar saboda rikicin da ya kunno kai.
Wike ya bayyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar a fadar gwamnati da ke Fatakwal.
“Za mu yi yakin a cikin jam’iyyar. Ba mu kamar su, lokacin da a 2014 suka fita daga Eagle Square. Sun manta. Sun fita suka koma APC.
Shugaban Ribas ya ce wadanda ke gudu daga fadan mutane ne marasa karfi kuma ba zai yi haka ba.
Gwamnan ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bayyana karara cewa dole ne a ware ofisoshin zabe da na jam’iyya.
“Kun dauki dan takarar shugaban kasa, kun dauki shugaban jam’iyya, kun dauki DG na yakin neman zabe. Muna magana ne kan siyasar jam’iyya.”
Wike ya ce dan takarar shugaban kasa, shugaban jam’iyyar da kuma DG na yakin neman zabe ne ke yanke hukunci.
“Kuna iya matsa wa shugaban BoT lamba ya yi murabus lokacin da wa’adin sa bai zo karshe ba. Amma ba za ku iya tursasa shugaban da ya yi murabus ba,” in ji shi.