Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce, shugabannin jam’iyyar PDP ba su tsunduma cikin yakin caccabar baka.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani martani da ya fito fili kan rikicin da ya kara kunno kai daga ‘ya’yan jam’iyyar daga zagin Gwamna Nyesom Wike ke kaiwa a kafafen yada labarai.
Tsagin Wike ya ci gaba da neman Iyorchia Ayu da ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
A kwanakin baya ne gwamnan jihar Ribas ya jagoranci wasu shugabannin jam’iyyar suka fice daga majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP bayan da Ayu ya ki yin murabus daga jam’iyyar.
Da yake jawabi a ranar Juma’a yayin bikin cikar jihar Akwa Ibom shekaru 35, Atiku wanda ya samu wakilcin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ce rikicin da ke cikin jam’iyyar rikici ne na siyasa wanda za a warware nan ba da jimawa ba.
Ya ce “ba mu da hannu ko kuma ba mu shiga yakin cin duri ba.
“Batun rashin jituwa ne na siyasa kuma nan ba da jimawa ba za a warware duk wannan kuma jam’iyyar PDP za ta ci gaba da dawwama har sai mun ci zabe da yardar Allah a watan Fabrairun 2023.