fidelitybank

Riƙaƙen ɗan ta’addan da ake zargi da kashe mutane 15 ya shiga hannu

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani dan ta’adda mai suna Suleman Iliyasu mai shekaru 28, wanda ya amsa laifin kashe mutane a kalla 15 a wasu hare-haren ‘yan bindiga a fadin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya gabatar da wadanda ake zargin ‘yan ta’addan da ake kira “Yar’bushiya” a gaban manema labarai a hedikwatar rundunar a ranar Talata.

Yar’bushiya ya kuma bayyana cewa ya taka rawa a wasu ayyukan fashi da makami, garkuwa da mutane da satar shanu da aka gudanar a kananan hukumomin Dandume, Faskari, Jibia, Batsari, da Kurfi na jihar Katsina.

Yar’bushiya, wanda ya yi ikirarin cewa ya fito daga Walawa Asaurara, Sabuwar Ungwa, karamar hukumar Jibia, Jihar Katsina, ya kuma bayyana cewa shi mamba ne na kungiyar ta’addanci ta Dankarami.

Dankarami wanda fitaccen dan ta’adda ne, ‘yan sanda na neman sa ne bisa laifin aikata laifukan cin zarafin bil’adama a fadin jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp