Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta samu rahotanin ƙarya fiye da 10,000 cikin kwana huɗu ta manhajar kai ɗaukin gaggawa da ta ƙaddamar mai suna Rescue Me App.
An ƙaddamar da manhajar ce, a shekarar da ta gabata don sauƙaƙa wa ‘yan sanda kai ɗaukin gaggawa a wuraren aikata laifuka wadda ke amfani da layin sadarwa na GPS ko kuma intanet.
Sai dai rundunar ta ce, ta rinƙs samun rahotanni na bogi daga jama’ar gari, abin da ke hana manhajar yin aiki yadda ya kamata.
Kakakin ‘yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce, tarin rahotannin na bogi da ke kan manhajar na haddasa mata damuwa da kuma kawo tsaiko.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi ƙorafin cewa, manhajar ba ta aiki yadda ya kamata. Sai dai ‘yan sanda sun ce, ta na aiki yadda ya kamata, amma akwai cunkoso a kanta na rahotannin bogi da ke jawo tsaiko.