fidelitybank

Remi ki faɗawa mijin ki Tinubu ƴan Najeriya na fama da yunwa – Sarkin Kano

Date:

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bai wa matar shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu sako zuwa mai gidanta wato shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sarkin ya nemi mai dakin Tinubu da ta isar da sakon da masarautar ta samu daga al’umma ga shugaba Tinubu cewa al’umma na fama da yunwa sakamakon tsadar kayan masarufi da ake fama da shi a wannan lokaci.

“Kayan abinci ya yi tsada. Mutane na shan wahala. Muna samun sakonni daga al’umma da muke shugabanta. Duk da cewa ba abu ne da ya fara yanzu ba. Amma tunda ku Allah ya dorawa shugabancin alhakin warware matsalar ya rataya a wuyanku,” in ji Sarkin Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi wannan magana ne a jiya Litinin a fadarsa yayin da matar shugaban kasar ta ziyarci fadar a birnin Kano.

Sarkin ya kara da cewa “sai kuma abu na biyu. Matsalar tsaro na addabar jama’a duk da cewa shi ma wannan ba lokacinku ya fara ba amma kasancewar su suke shugabanci to su ne Allah ya dorawa nauyin.”

Daga karshe mai martaba Sarkin na Kano ya nemi da gwamnatin tarayya ta waiwayi batun dauke wani sashe na babban bankin kasa da hukumar da ke sanya ido kan tashi da saukar jirage ta kasa daga Abuja zuwa birnin Legas.

“Muna kira ga shugaban kasa da a waiwayi wadannan batutuwa idan akwai kuskure sai a gyara”. In ji Alhaji Aminu Ado Bayero.

Sarkin ya ce sakon zai fi saurin zuwa kuunuwan shugaban kasancewar uwargidansa aka bai wa

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp