Kungiyar Real Madrid wadda ta zama gwarzuwa har sau 13 a gasar zakarun kungiyoyin Turai za ta kara da Chelsea da ta lashe gasar a bara.
Manchester city za ta kara da Atletico Madrid, yayin da Liverpool za ta barje gumi da Benfica sai kuma wasan Bayern munich da Villarreal.
Za a buka wasannin a ranar 5 da 6 ga watan Afrilu sai kuma 12 da 13 ga Afrilun wannan shekarar.
Za kuma a fafata a wasan kusa da na karshe a ranakun 26-27 sannan a buga na biyu a ranar 3-4 ga watan Mayu mai zuwa.
Za a buga wasan karshe na gasar a filin wasa na Stade de France da ke Faransa a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, bayan dauke shi da ka yi daga St Petersburg bayan fara mamayar Rasha a Ukraine
Wannan na nufin Chelsea za ta sake haduwa da tsohon kocinta Carlo Ancelotti, wanda ya lashe gasar Premier sau biyu a shekara biyun da ya yi yana tafiyar da kungiyar tsakanin 2009 zuwa 2011.
Dan kasar Italiyan na daya daga cikin kociyoyin Itakiya da ya lashe Champions sau uku, lokacin da yake Real madrid a 2014, kungiyar da ya sake komawa kungiyar a bara da ya bar Everton.
Chelsea da Real madrid sun hadu a wasan kusa da na karshe a bara, yayin da kungiyar ta Thomas Tuchel ta cire Madrid da jimillar kwallaye 3-1 ta doke Manchester City a wasan karshe.
Atletico Madrid ta samu damar haduwa da Manchester biyu a wasa guda, bayan ta doke United da ci 2-1 a zagayen ‘yan 16.
Wannan ce fafatawar farko da za a yi tsakanin ATM da City wadda ta lallasa Sporting Lisbon da ci 5-0 a jimillar kwallaye da aka ci a wasanni biyu.
Liverpool kuma ta buga wasa da kungiyar Portugal Benfica 10 a gasar Turan, haduwar da aka yi ta karshe ita ce wadda aka yi 5-3 a wasan kusa da na karshe a 2010.
Jurgen Klopp na neman hada kofina hudu a wannan kakar, kuma tuni ya lashe kofin Carabao kuma ana fafatawa da shi a FA Cup da gasar Premier.
Wasa kusa da daf da na karshe
Chelsea da Real Madrid
Manchester City da Atletico Madrid
Villarreal da Bayern Munich
Benfica da Liverpool