Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta tabbatar da cewa, dan wasanta na kasar Brazil Reinier Jesus, ya bar kungiyar zuwa Girona FC.
Real Madrid ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na yanar gizo ranar Juma’a gabanin wasansu da Celta Vigo a gasar La Liga ranar Asabar.
Sanarwar ta Real Madrid ta ce, “Real Madrid CF da Girona FC sun amince da aro dan wasan Reinier na wannan kakar, har zuwa 30 ga Yuni, 2023.”
Jesus ya kulla yarjejeniya da Real Madrid daga kungiyar Flamengo ta Brazil kan kudi fan miliyan 25 a shekarar 2020.


