Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu babban rauni a karawar da za ta yi da Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai ranar 9 ga watan Mayu.
Dan wasan Real Madrid Luka Modric ya samu rauni a kafarsa ta hagu.
Dan wasan na Crotia ya fafata da Girona a ranar Talata kuma nan take aka shafa kankara a cinyarsa bayan ya ji zafi sosai.
Real Madrid ta fitar da wata sanarwa game da raunin da Modric ya samu, inda ta ce, “Bayan gwajin da hukumar kula da lafiya ta Real Madrid ta yi wa Luka Modrić, an gano raunin da ya samu a bayan cinyarsa ta hagu. Za a sanya ido a kan ci gaban da ya samu.”
A halin da ake ciki, kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce a taron manema labarai kafin wasan da kungiyarsa za ta yi da Almeria a ranar Asabar: “Luka Modric ya ji rauni. Ba mu san lokacin da zai dawo ba, za mu ga wasan karshe na Copa del Rey – ba mu sani ba. ”
Har yanzu dai babu tabbas ko Modric zai dawo nan da lokaci don buga wasanni hudu masu zuwa da Real Madrid da Almeria da Real Sociedad da Osasuna da kuma Manchester City.