Jami’in tattara sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Ribas, Farfesa Charles Adias, ya dage tattara sakamakon zaben na ranar Asabar.
Adias ya dage taron tattara sakamakon zabe a jihar, bisa zargin barazanar da wasu magoya bayan jam’iyyar da ba a bayyana sunayensu ba suka yi na yi wa rayuwarsa.
Mataimakin shugaban jami’ar tarayya, Otueke ne ya sanar da dage taron a safiyar ranar Talata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar tattara bayanai na jihar da ke Fatakwal, babban birnin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan zaben shugaban kasa na jihar Ribas, Aderemi Adeoye, ya bukaci jami’in tattara sakamakon zaben ya bayyana sunayen wadanda ke barazana ga rayuwarsa.
Duk da haka, Adias ya dage cewa ba zai ci gaba ba har sai Kwamishinan Zabe na jihar ya yi magana game da wasu batutuwan wadanda ke yi masa barazana, da kuma na’urar tantance masu kada kuri’a ta Bimodal, BVAS.
Kafin sanarwar nasa, an tattara sakamako daga kananan hukumomi 21, amma kananan hukumomi biyu – Obio-Akpor da Degema suna kan gaba.