Janar Abdulrahman Dambazau, tsohon babban hafsan soji kuma ministan harkokin cikin gida, ya yi zargin cewa ‘yan ta’adda da mambobin haramtacciyar kasar Biyafara, IPOB, za su zama babbar barazana ga babban zabe a 2023.
Dambazau ya yi magana ne ranar Talata a Abuja a taron shekara-shekara na Jaridar Blueprint mai taken, “Siyasa ta 2023: Tsaron Kasa da Zaman Lafiyar Najeriya”.
Ya yi imanin cewa rashin tsaro zai yi tasiri a zaben 2023, yana mai cewa har yanzu wasu al’ummomi za su bar muhallansu, kuma ‘yan ta’adda za su ci gaba da kai hare-hare a wurare masu laushi don hana ‘yan Nijeriya kada kuri’unsu.
A cewarsa, “Jami’an INEC da ma’aikatan wucin gadi za su kasance cikin fargaba sosai duk da tabbacin da gwamnati ta ba su na kare su. Samun damar zuwa rumfunan zabe a cikin al’ummomin kan iyaka na iya haifar da wasu matsaloli. Wannan shi ne karin dalilin da ya sa dole a samar da isasshen tsaro.”


