Shugaban hukumar ta NCFRMI, Tijjani Aliyu, shi ya bayyana haka lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Katisna Dikko Radda ziyara a ranar Juma’a.
Ya ce zuwa 2022, hukumar tana da mutum sama da miliyan uku waɗanda ambaliya da bala’o’i suka ɗaiɗaita, inda ya ce a yanzu an samu ƙaruwar mutanen da suka ɗaiɗaita da kashi 100.
“A yau zan iya cewa, muna da ƴan Najeriya da ba su kasa miliyan 6.1 waɗanda suka rasa gidajensu.
“Ya kamata a nemo hanyar koyawa waɗannan mutane sana’o’i da kuma ba su horo, saboda su dogara da kansu nan gaba, domin gwamnati ba za iya ci gaba da kula da dukkansu ba,” in ji Aliyu.
Ya ƙara da cewa hukumar tana yunkurin kafa cibiyoyi guda uku na koyon sana’o’i a faɗin arewa maso gabas.
Ya ce ya kai ziyarar ce domin raba abinci ga mutane sama da 700 waɗanda aka ɗaiɗaita a jihar ta Katsina.
Ya kuma ce sun horar da mutum 120, da kuma bai wa iyayensu da suka kai 70 kayakin yin sana’o’i domin kyautata rayuwarsu.
Har ila yau, ya ce sun gina gidaje a yankunan da sansanonin ƴan gudun hijira suke, musamman ga waɗanda ba su da ra’ayin komawa garuruwansu na asali.


