Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa, tuni ya rubuta wasiyyarsa, ko bayan babu ransa, sakamakon hauhawar rashin tsaron da ya addabi Najeriya.
Kamar yadda aka san gwamnan da batun rashin tsaron kasar nan, gwamnan ya ce, ya na da tabbacin cewa, iyalansa ba za su yi fada kan gadon da ya bar musu ba, idan wani abu ya faru da shi.
Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da ya karbi wakilan Administrative Staff College of Nigeria (ASCON) wadanda suka samu shugabancin darakta janar, Misis Cecilia Gayya a gidan gwamnatin jihar da ke garin Makurdi.
Ya ce, “Tuni na rubuta wasiyyata. Ba na tsoron kowa. Idan na mutu yanzu, na san iyalina ba za su fada a kan abinda na bar musu na gado ba. Na riga na fadi abinda nake so. Da kuma jama’ar da ke shiru a kan abinda ke faruwa a kasar Najeriya, ina son sanar da su cewa, suna da ‘ya’ya. Tabbas, shiru kamar yarda ce. Domin haka, dole ne ‘yan Najeriya su jajairce kan lamarin nan”. A cewar Ortom.