Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a jihar saboda barazanar tsaro.
Kwamishinan ilimi na jihar Dr. Lawan Yunusa Danzomo ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin sa.
Danzomo ya bayyana cewa wannan umarni bai kebanta da jihar Jigawa ba, a’a duk jihohin ne musamman jihohin da ke kan iyaka.
Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare ba tare da bata lokaci ba a lokacin da daliban ke zana jarabawar kammala karatunsu.
Rufewar ba zato ba tsammani ya haifar da firgici tsakanin mazauna yankin, dalibai da malamai.
Wani shugaban makarantar ya shaidawa jaridar DAILY POST cewa, an bukaci su rufe makarantun tare da sakin daliban nan take.


