An dage shari’ar dan Chanan da ya kashe budurwarsa Ummita a jihar Kano.
An dai dage zaman kotun ne har zuwa ranar 27 ga watan Oktoba, har sai an samarwa da Mr. Geng Quangrong, wanda zai yi masa tafinta daga turanci zuwa Chanisanci.
Ba a jima da fara zaman kotun ba ne aka dage zaman, saboda matsalar rashin fahimtar bayanai daga bangaren Mista Geng, wanda ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari, da aka fi sani da Ummita, a Kano.