fidelitybank

Rashin shaidu 3 ya hana Abba buɗe kariyar sa a kotun zaɓe

Date:

Rashin halartan shaidu uku a ranar Juma’a ya hana Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) bude kariyarsa a kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano.

APC na kalubalantar INEC kan ayyana dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Wadanda suka amsa karar a gaban kotun sun hada da INEC, Yusuf da NNPP.

Da aka kira karar, Lauyan Yusuf, Mista Eyitayo Fatigun SAN, ya shaida wa kotun cewa shaidu ukun da suka gayyata ba su halarta ba.

“Muna ba da hakuri saboda shaidu ukun sun samu matsalar jirgin da zai tashi zuwa Kano daga Abuja. Muna neman a dage zaman,” in ji Fatigun

Lauyan INEC, Emmanuel Osayomi da Lauyan NNPP, John Olusola SAN, ba su yi adawa ba.

Shi ma lauyan wanda ya shigar da kara, Offiong Offiong SAN, bai yi adawa da bukatar dage shari’ar da wanda ake kara na biyu ya yi ba.

NAN ta ruwaito APC a ranar 15 ga watan Yuli, ta rufe karar ta, bayan ta kira shaidu 32, yayin da INEC ta rufe karar ta a ranar 21 ga watan Yuli.

Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ya dage sauraron karar har zuwa ranar Asabar domin jam’iyyar NNPP ta bude karar.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp