Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ya bukaci al’ummar jihar da su kara kaimi wajen addu’o’in samun sauki ga gwamna Oluwarotimi Akeredolu.
Oladiji, wanda ya bukaci jama’a da kada su yanke kauna, ya yi kira da a daina yada jita-jitar da ake ta yadawa game da halin da gwamnan ke ciki.
Kakakin ya bayyana haka ne a yayin wata addu’a ta musamman da aka shirya wa gwamnan a cocin Saint Andrew Cathedral Church, Owo.
An gudanar da taron addu’o’in ne a mahaifar sa ta Owo, hedikwatar karamar hukumar Owo ta jihar.
Idan dai za a iya tunawa dai an yi ta cece-kuce kan halin da lafiyar gwamnan ke ciki, inda lamarin ya haifar da tashin hankali a jihar.
Oladiji, wanda aka fi sani da Landmark, da mataimakinsa, Akinruntan Abayomi; Ogunmolasuyi Oluwole (shugaban masu rinjaye); da Tosin Ogunlowo (Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye) sun halarci zaman addu’ar.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Raymond O. Daudu (Mataimakin Shugaban marasa rinjaye) da Victor Japheth (Mataimakin Cif Whip), da sauransu.