fidelitybank

Rashin kuɓutar da ‘yan Chibok ba laifin Buhari ba ne – Gwamnati

Date:

Fadar shugaban ƙasa ta ce, kada ƴan Najeriya su ɗora wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari laifin rashin kubutar da dukkan ƴan matan Chibok da aka yi garkuwa da su.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar yaɗa labarai, Femi Adesina, shi ya bayyana haka yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily yau Alhamis.

“A 2015, mun san yadda Najeriya take, a yau kuma mun san inda muke. An yi garkuwa da ƴan mata 267, kusan 57 sun tsere nan take sannan gwamnati ta dawo da sama da 100,” in ji Adesina.

Ya ce waɗanda suka rage ba su fi 90 ba, kuma suma suna da hakki na kuɓutar da su domin dawowa gida.

“Sai dai, idan gwamnati ta zo kan mulki lokacin da aka sace ƴan matan kuma gwamnati mai ci ba ta iya bin diddigin ina aka kai su ba, to ba za ka ɗora wa sabuwar gwamnati laifin rashin dawo da su ba, hakan bai kamata ba. A sace ɗaliban Dapchi a karkashin gwamnatinmu, an dawo da su a cikin mako ɗaya in ban da guda biyar ba ciki har da Leah Sharibu,” in ji Adesina.

Mai baiw a shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai ya ce gwamnati na ɗaukar tsauraran matakai wajen dakile ayyukan masu garkuwa a duk lokacin da aka samu afkuwar hakan, inda ya ce gwamnati mai zuwa ma ta ɗauki nauyi wajen ganin an ƙara kuɓuto da sauran ƴan matan.

Ya ce ya kamata a gode wa gwamnati mai barin gado kan irin ci gaban da ta kawowa ƙasar.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp