Sabon dan wasan gaban kungiyar Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang, ya ce rashin jituwa ne tsakanin sa da mai horas da Arsenal, Mikel Arteta, ya sanya barin kungiyar.
A ranar Laraba ne dan wasan Gabon wanda ya kammala cinikinsa kyauta zuwa Barcelona.
Tafiyar Aubameyang ya biyo bayan tsige shi daga mukamin sa na kyaftin a Arsenal, wanda hakan ya ki yi masa dadi a kungiyar ta kai ya fara ajiye shi a benci.