A karon farko tun bayan ficewarsa daga Jamhuriyar Nijar, Jakadan Faransa, Sylvain Itté, ya tattauna da gidan talabijin na ƙasar Faransa a ranar Alhamis.
Ya ce ya yi matuƙar gajiya bayan da ya kwashe wata biyu cikin tashin hankali da fargaba.
Ya bayyana juyin mulkin a matsayin wani “gagarumin rashin hankali” kuma “babu wanda ya yi nasara”.
“Wannan lamarin abu ne na cikin gida tsakanin shgaban ƙasa wanda ya ɗauki aniyar yaƙi da rashawa da kuma wasu manyan sojoji waɗanda ke adawa da hakan.” In ji Jakadan
Jakadan ya ƙara da cewa “Shugabannin sojin sun dakatar da masu kawo wa ofishin jakadancinmu kaya, ta hanyar yi amsu barazana. Ko abinci da ruwa sai ta ɓoyayyar hanya ake shigar mana da su.”
Ya kuma yi ƙarin haske kan zanga-zangar da ƴan Nijar suka yi a gaban ofishin jakadancin Faransar da ke Nijar a ranar 30 ga watan Yuli, kwanaki kaɗan bayan juyin mulkin.
“Masu zanga-zangar sun kwashe sa’o’i biyu da minti 30. A wannan ranar dukkan mu mun shiga cikin hatsari mun kuma kusan haɗuwa da haɗari, saboda mutane sama da 6,000 ne suka fito domin yin faɗa da mu, kuma sun je ne da niyyar fasa ofishin.”