Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu a ranar Alhamis ya ce, matsalar Najeriya ba cin hanci da rashawa ba ce illa rashin hadin kai da hadin kan al’umma.
Ikpeazu ya bayyana hakan ne a wajen taron gabatar da wani littafi ga jama’a a Abuja.
Ya ce babbar matsalar Najeriya ba ita ce tsaro ko tattalin arziki ba.
Karanta Wannan: El-Rufa’i ya yi watsi da kalaman Buhari akan tsofaffin kudi
“Rashin hadin kai ne. Rashin haɗin kai ne. Matsalarmu ita ce zargin juna da rashin mutunta juna.” Yace
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ganin kasar ta kowa ce a karkashin Allah daya, ya kara da cewa domin gina kasar dole ne ‘yan Nijeriya su hadu ba tare da la’akari da kabila da addini ba.