Ƙungiyoyin farar hula a Najeriya ciki harda CISLAC sun yi alla-wadai da matakin da ƙasar Ukraine ta ɗauka na kiran ƴan Najeriya da Afrika su taimaka mata da mutane, domin yaƙar Rasha.
Shugaban kungiyar CISLAC, Awwal Musa Rafsanjani, a tattaunawarsa da BBC cikin yanayi na nuna takaci ya ce, sam matakin bai dace ba.
Ya ce, ”Wannan kira da Ukraine ta yi wa kasashen Afrika, domin shiga yakin da ba su ji ba, ba su gani ba. Sam wannan bai dace ba, abin takaicin ma shi ne kafin ka je ka kai kan ka halaka sai ka biya dala 1,000 idan aka sauya zuwa kudin Najeriya ana maganar Naira 575,000.
“Ina ganin wannan rashin sanin ciwon kai ne ga ‘yan Najeriya, kuma gwamnati na da laifi wajen rashin fitowa ta nunawa ‘yan kasa illar da ke cikin wannan kasada.
“Ya dace ma’aikatar harkokin waje ta fito ta yi bayani dalla-dalla da gargadin ‘yan Najeriya kar su sanya kan su cikin abin da babu ruwansu a ciki, rigimar da ba ta shafe su ba, babu kuma wani alfanu da za su samu idan sun tsoma baki a ciki, abin ba zai amfani kasarsu da ma Afirka baki daya ba,” in ji Rafsanjani.
Ita ma ƙasar Senegal ta yi watsi da wannan umarni na Ukraine cewa, ya saɓa wa dokar ƙasar ta, sai dai kuma tuni mutane 36 a ƙasar su ka nuna sha’awar taimaka wa Ukraine, yayin da a Najeriya matasa sama da 100 su ka miƙa sunan su da adireshi da email a ofishin jakadancin Ukraine