Ma’aikatar ilimi ta Rasha ta sanar da cewa, za a fara wayar da kan ɗaliban firamare kan dalilin da ya sa ya zama dole ƙasar ta ƙaddamar da yaƙi a Ukraine.
Sanarwar ta ce, za a bai wa ɗaliban darasin ta intanet da misalin ƙarfe 12:00 agogon ƙasar (10:00 agogon Najeriya da Nijar) na yau Alhamis.
Za a bai wa masu kallo darasi “kan barazanar da ƙawancen tsaro na Nato ke yi wa ƙasarmu da kuma dalilin da ya sa Rasha ta tsaya wajen kare fararen hula yankunan Donetsk da Luhansk”.
Kazalika, sanarwar ta ce, yaran za su koyi yadda za su tantance gaskiya da ƙarya, saboda yawan labaran da suke samu da hotuna da bidiyo a intarnet. In ji BBC.