Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce zai kafa wata tashar nukiliya mai cin gajeran zango a Belarus da ke kawance da ita nan da watanni masu zuwa.
Ya ce makamin Iskander-M na da karfin daukar kananan makamai da kuma manya.
Makaman da Rasha za ta kafa a Belarus za su iya cin kilomita 500.
Da yake bayani a St Petersburg, Putin ya ce kasarsa za ta taimakawa Belarus wajen habbaka jiragen yakinta, musamman kirar SU-25.
Zaman doya da manja na kara ta’azzara tsakanin Rasha da kasashen Yamma tun bayan kutsen da Rasha ta yi a Ukraine.