Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa za ta girke makaman nukiliya a maƙabciyarta Belarus.
Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ruwaito Mista Putin na cewa matakin ba zai saɓa wa yarjejeniyar ƙasa-da-ƙasa ta taƙaita yaɗuwar makaman nukiliyar ba, kamar yadda Amurka ta girke nata makaman a nahiyar Turai.
Shugaba Putin ya ce Rasha ba za ta mayar da ikon sarrafa makaman zuwa Belarus ɗin ba.
To sai dai Amurka ta bayyana damuwarta game da matakin, tana mai cewa ba ta ga dalilin yin hakan ba, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin tsaron ƙasar ta fitar.
Amurkan ta ce a shirye take wajen kare tsaron ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO.
Ƙasar Belarus dai ta haɗa iyaka da Ukraine, da kuma ƙasashen Polan da Lithuania da Latvia, waɗanda mambobin NATO ne.
Wannan shi ne karon farko tun shekarun 1990, da Rasha za ta girke makamin nukiliyarta a wata ƙasar.
Bayan wargajewar tarayyar Soviet a shekarar 1991, duka makaman da ke ƙasashen Ukraine, da Belarus da kuma Kazakhstan – waɗanda duka suka samu ‘yancin gashin kai – an mayar da su zuwa Rasha a shekarar 1996.
Belarus ta kasance babbar ƙawar Rasha da ke goyon bayan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. In ji BBC.
A wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasar ta talbijin ranar Asabar shugaba Putin ya ce shugaban Belarus Alexander Lukashenko, ya daɗe yana kiran Rasha da ta girke makaman nukiliyarta a ƙasarsa.