Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa Rasha barazana ce ga Turai baki ɗaya ba Ukraine kaɗai ba.
Mista Merz ya yi gargaɗin cewa, Moscow na tasiri a lamuran da suka shafi zaman lafiya da yanci kai da tsarin siyasar Turai.
Mista Merz ya ce shi da shugaba Trump suna aiki tare domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Shugaban gwamnatin ta kuma sake nanata kalaman cewa ƙasashen Turai na buƙatar su iya kare kansu a kodayaushe.
Ya ce a a halin da ake ciki yanzu gwamnatin Jamus ta soma kashe makudan kuɗaɗe wajen inganta ɓangaren tsaron ƙasarta.