Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana kisan da aka yi wa fursunonin yaƙi 50 a wajen da ake tsare da su a bangaren da Rasha ta mamaye a yankin Donesk a jiya Juma’a a matsayin laifin yaki.
A cikin jawabin da ya saba yi ga kasar a kullum,Mr Zelensky, ya kuma yi kira da a ayyana Rasha a matsayin mai goyon bayan ta’addanci.
Ita ma ana ta ɓangaren, Rasha ta zargi Ukraine din da kashe fursunoni a wani harin roka da ta kai.
Ukraine dai ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar agaji ta Red Cross a kan su gudanar da bincike a game da kisan.
Shugaban tsare-tsare a kungiyar tarayyyar Turai Joseph Borrell, ya ce, kungiyarsu na goyon bayan duk wani bincike da za a yi a game da batun take hakkin dan adam da aka aikata a yayin abin da ya kira hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine.