Shugaban Ukraine Volodomyr Zelensky, ya ce, kasarsa za ta yi nasara a yakin da take yi da Rasha.
A wani jawabi da ya yi ta bidiyo, inda yake Allah-wadarai da zargin da ake yi cewa Rasha na harin fararen hula.
Kalaman na Mista Zelensky, sun biyo bayan sanarwar da babban mai gabatar da kara na Ukraine ya yi ne cewa, an gano gawarwakin mutane fiye da dari hudu daga garuruwan da ke kusa da babban birnin kasar Kyiv, wadanda Rasha ta yi wa kisan gilla.
A jawabin da ya gabatar cikin jimami da kalamai masu sosa rai ranar Lahadi da daddare Shugaba Volodomyr Zelensky, ya zargi Rasha da aikata laifin kisan kiyashi a kan ‘yan Ukraine da ke kananan garuruwan da ke kewaye da babban birnin kasar, Kyiv.
Garuruwan da suka hada da Bucha da Irpin da kuma Hostemel, yana mai tambayar dalilin yi wa wadannan mutane da ba su ji ba, ba su gani ba kisan gilla.