Rasha ta yi kira ga dukkan ɓangarori da su yi taka-tsantsan da kuma nuna damuwarsu kan yaɗuwar rikici bayan da Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa Isra’ila cikin dare.
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar cewa “Mun dogara ga ƙasashen yankin wajen ganin sun magance matsalolin da ake fama da su ta hanyar siyasa da diflomasiyya.”
Moscow ta kara da cewa sau da dama ta yi gargaɗin cewa kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kasa mayar da martani mai kyau game da harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a ƙasar Siriya, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’ai bakwai na dakarun juyin-juya halin Iran da suka haɗa da manyan kwamandoji.
Hakan na zuwa ne bayan da Amurka da Birtaniya da Faransa suka nuna adawa da sanarwar da Rasha ta rubuta wa kwamitin sulhu na MDD wanda zai yi Alla-wadai da harin da aka kai harabar ofishin jakadancin Iran a Syria.
Iran ta zargi Isra’ila da kai wannan harin, amma Isra’ilar ta ce ba ta cewa uffan kan rahotannin ƙasashen waje.