Jami’ai a Ukraine sun ce an sake kai hare da jirage marasa matuki a babban birnin kasar Kyiv.
Hukumomi sun ce sojojinsu na sama na aiki tuƙuru a kai amma duk da haka hare-haren sun shafi wasu wurare da dama.
Kazalika akwai rahotannin da ke cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a birnin Mariupol.
Bayanai sun ce abubuwan sun fashe ne a filin jirgin saman birnin na Mariupol, inda sojojin Rasha suke.