Jami’an Rasha sun ce, an tabbatar da mutuwar shugaban kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin bayan da aka yi wa gawarwakin mutanen da ke cikin jirgin gwajin Æ™wayoyin halitta
Tawagar masu binciken sun ce gwajin da suka yi wa gawarwaki 10 da ke cikin jirgin, ya yi dai dai da na sunayen fasinjojin ke cikin jirgin.
A ranar 25 ga watan Agusta ne jirgin Prigozhin ya faÉ—i a arewa maso yammacin birnin Moscow, tare da kashe duka mutanen da ke cikinsa.
Gwamnatin Rasha ta musanta raÉ—e-raÉ—e radin da ake yaÉ—awa cewa tana da hannu a faÉ—uwar jirgin.
Cikin watan Yuni ne Mista Prigozhin ya jagoranci wani boren soji da bai yi nasara ba, ga gwamnatin shugaba Putin na Rasha


