Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce, shugaban Rasha Vladimir Putin na cikin tsaka mai wuya bayan Amurka da Birtaniya sun sanya wa fannin makamashin Rasha sabbin takunkumi kan mamayar Ukraine.
Mista Biden ya shaida wa manema labarai a Fadar White House ce wa abu ne mai matukar muhimmanci a tabbatar ba a bai wa shugaban na Rasha sararawa ba.
Shugaban Amurkan ya ce takunkumin da aka sanya wa Rashan, zai girgiza tattalin arzikinta ta yadda zai yi mata wahalar iya ci gaba da yaƙin Ukraine ba.
Tun da fari ma’aikatar cikin gida a Amurka ta fitar da bayanan yadda takunkuman za su shafi ƙasar, ciki har da jiragen ruwa kusan 180.