Daren da Rasha ta shafe tana kai hare-hare ta sama ya sa Rashar ta yi illa ga yankin Pozniake da ke Kyiv babban birnin ƙasar.
Manyan gine-gine da ke yankin sun kama da wuta inda tagogi suka yi ta fashewa.
Masu aikin kashe gobara sun ta ƙoƙari cikin hayaƙi da ɓaraguzai domin kashe gobarar da ta tashi a daidai lokacin da ake samun fashewar abubuwa a cikin birnin.
Aƙalla mutum takwas aka raunata a Pozniake. Ɗaya daga cikin mazaunin birnin ya bayyana cewa, “Putin, muna so mu ga an yanka ka kamar dabba.”
A wasu wuraren, sararin samaniya a cikin dare ya turnuƙe da hayaƙi sakamakon tashe-tashen bama-bamai.