Shugaba Volodymyr Zelensky, ya ce, sojojin Rasha sun lalata yankin gabashin Donbas da ke Ukraine gaba daya.
A cikin jawabinsa na bidiyo na dare, Mista Zelensky ya bayyana halin da ake ciki a Donbas a matsayin mummuna, yana mai zargin Rasha da kai hare-haren bama-bamai.
A jawabin na kullu yaumin ya kuma kara da cewa Ukraine na ci gaba da kwato wasu birane a kusa da Kharkiv.
Rasha dai ta mayar da hankali kan yankin Donbas, wanda ya kunshi lardunan Donetsk da Luhansk inda ‘yan awaren da ke samun goyon bayan Moscow suka kwashe shekaru suna fafatawa da sojojin Ukraine.